Rwanda ta amince da karbar 'yan gudun hijira 250 daga Amurka
August 5, 2025Rwanda ta amince da karbar bakin haure 250 daga Amurka, kamar yadda gwamnatin Amurka ta sanar a wannan Talata, sakamakon tsauraran matakan korar baki marasa cikakkun takardu da shugaba Donald Trump ya dauka.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin Rwanda Yolande Makolo ta fitar, ta tabbatar da cimma wannan yarjejeniya, ko da yake babu karin bayanin ranar da za ta karbi mutanen.
Karin bayani:Rwanda da DRC sun tattauna bayan alkawarin zaman lafiya
Amurka ta dage wajen kulla yarjejeniya da kasashen Afirka da za su amince da karbar 'yan gudun hijirar da ke makale a kasar ba bisa ka'ida ba, tun bayan ikirarin Mr Trump na cewar irin wadannan mutane sun cika kasarsa.
Karin bayani:MDD ta yi gargadi kan rikicin Kwango
Tuni Amurkar ta aike da mutane 13 zuwa kasashen Sudan ta Kudu da kuma Eswatini, kuma ta kori daruruwan bakin haure 'yan asalin kasashen Venezuela da Costa Rica da El Salvador da kuma Panama.