Rwanda da DRC sun tattauna bayan alkawarin zaman lafiya
August 1, 2025Rwanda da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo sun gudanar da taro na farko na kwamitin sa'ido na hadin gwiwa a ranar Alhamis, a matsayin wani mataki na aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da suka kulla a watan da ya gabata a birnin Washington na Amurka.
Ko da yake akwai wasu abubuwan da har yanzu ba a kai ga cimmusu ba a yarjejeniyar.
Kwango da M23 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu
Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da Qatar da Amurka sun halarci wannan taron a Washington, wanda aka yi domin aiwatar da yarjejeniyar da kuma warware sabani da ke tsakanin kasashen biyu.
Yarjejeniyar da aka cimma a watan Yuni tsakanin Rwanda da Congo ta kasance wani gagarumin ci gaba a tattaunawar da gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump ta jagoranta.
An halaka mutane da dama a wata majami'a da ke DRC
A cikin yarjejeniyar da aka cimma a Washington, kasashen biyu na Afirka sun yi alkawarin janye sojojin Rwanda daga gabashin Congo cikin kwanaki 90.