Ruwanda ta yi watsi da zargin taimaka wa M23
August 11, 2025Shugaban Hukumar Kare Hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk ya nuna kaduwarsa kan rahoton da ya nuna cewa, 'yan tawayen M23 sun kashe fararen hula a kalla 319 a watan Juli duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma, yayin da kuma ake ci gaba da gudanar da tattaunawar zaman lafiya.
Karin bayani: Ruwanda: Ko karshen rikici da Kwango yazo?
Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya ce an kashe mutanen ne a arewacin Lardin Kivu, kana ya zargi dakarun Ruwanda da taimaka wa 'yan tawayen. Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Ruwanda ta ce ba za ta amince da danganta ta da harin da ita ma ta yi Allah wadai da shi. A watan Junin wannan shekarar ce a aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Kwangon da M23 a Dohayayin da aka sake sanya hannu kan wata birnin Washinton na Amurka.