Ruto na kenya ya yi kakkausar suka kan shirin zanga-zanga
June 22, 2025Shugaban kasar Kenya William Ruto ya caccaki ‘yan adawar kasarsa kan shirinsu na gudanar da zanga-zangar cika shekara daya da fara tarzomar neman sauyi. Masu fafutuka da iyalan wadanda aka kashe sun sha alwashin gudanar da wata sabuwar zanga-zanga a ranar 25 ga watan Yuni a matsayin ranar tuna baya, inda suka bukaci 'yan sanda da jami'an gwamnati da su kyale su, su gudanar da ita cikin lumana.
Karin bayani: Matasan Kenya da kafar sada zumunta
Sai dai a lokacin da yake tsokaci a gundumar Meru, Shugaba Ruto ya zargi abokan hamayyarsa da yin amfani da kalaman son kai da farfaganda wajen shafa wa gwamnatinsa kashin kaji. Dama dai a makon da ya gabata, an sake samun karin zanga-zanga a kasar Kena da ke gabashin Afirka saboda yawaitar cin zarafi daga 'yan sanda.
karin bayani: 'Yan sanda na murkushe zanga-zanga a Kenya
Idan za a iya tunawa dai, zanga-zangar da aka yi a bara ta haifar da rikicin shugabanci a gwamnatin Ruto, lamarin da ya tilasta masa dakatar da wani bangaren na dokar karin haraji tare da yin garambawul ga majalisar ministocinsa.