SiyasaArewacin Amurka
Rushdie zai fitar da sabon littafi tun bayan kai masa hari
March 27, 2025Talla
Salman Rushdie zai saki littafin a ranar 4 ga watan Nuwambar 2025, littafin na kunshe da wasu daga cikin gwagwarmayar da ya sha ciki har da yunkurin halaka shi da Hadi Matar ya yi a birnin New York na Amurka. Harin da aka kai masa a shekara ta 2022, ya yi sanadiyyar tsiyayewar idonsa guda.
Karin bayani:An tuhumi wanda ya yi yunkurin kashe Salman Rushdie
Lauyoyin da ke kare Mr. Matar sun bayyana cewa harin da ya kai wa Mr. Rushdie bai da alaka da fatwar da kasar Iran ta bayar a 1989, na bada tukuici ga duk wanda ya kashe marubucin sakamakon kalaman batanci da ya yi kan addinin Islama, a mukalar da ya fitar mai suna "The Satanic Verses", wanda ya haifar da mummunar martani daga kasashen musulmi.
.