Robert Habeck ya yanke kauna da jagorantar Greens
February 24, 2025A cikin tattausar lafazi Mr. Habeck ya shaidawa manema labarai cewa jam'iyyar The Green ta fadi kasa warwas da kashi 11.6 bisa 100 sabanin tagomashin da jam'iyyar ta samu a zaben 2021, inda ta samu kashi 14.7 bisa 100. Ya kuma kara da cewa wannan ba sakamako bane mai kyau da jam'iyyar za ta yi tinkaho da shi.
Karin bayani: Jam'iyyar the Greens, na son sake sabon lale
Rashin nasarar jam'iyyar Greens na nufin cewa Robert Habeck zai rasa mukaminsa a gwamnati, kasancewar Friedrich Merz na kawancen jam'iyyar CDU/CSU shi ne zai kafa gwamnati tare da kawancen jam'iyyar SPD ta Shugaban Gwamnatin Jamus mai barin gado Olaf Scholz.
Karin bayani: Jamus: The Greens ta amince da shirin kafa gwamnati
Mr. Habeck da sauran jagororin jam'iyyar The Greens sun yi amannar cewa duk da rashin nasarar da jam'iyyarsu ta fuskanta a zaben, ta dara jam'iyya mai mulki ta SPD wacce ta samu mummunar koma baya a tarihinta.