Rikicin gabashin Kwango na daukan hankali
February 28, 2025Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na bukatar tattaunawa ta neman sulhu wannan shi ne taken da Jaridar taz die Tageszeitung ta wallafa sharhinta a kai.Yakin gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na barazanar wa zaman lafiya a yankin Gabashin Afirka. Tuni da mutane dubu 400,000 suka rasa matsugunansu sannan an kashe dubai.
Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun ce a Goma kadai kimanin mutane dubu-2900 aka kashe yayin da 'yan tawyen suka karbe iko da daukacin lardin Arewacin Kivu, yanki mai arzikin albarkatun kasa wanda girmansa ya kai kamar girman kasar Switzerland, wanda a ciki kusan mutane miliyan shida ne ke rayuwa.
Karin Bayani: Sharhin Jaridun Jamus a kan nahiyar Afirka
Jaridar ta Tageszeitung ta ce da wahalla 'yan tawayen su janye tun da har sun kafa gwamnatinsu da ke kalubalantar gwamnatin Kinsasha. Sai dai kawai lallaba, Sai dai a yi fatan kwamiti na wasu dattawan Afirka guda uku da Kungiyar kasashen Kudancin Afirka ta kafa wato SADC wadanda suka hada tsohon Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, da Olusegun Obasanjo tsohon shugaban Najeriya da tsohon firaministan Habasha Hailemariam Desalegn sun samar da mafita a rikicin na Kwango. Wanda ba lallai ba ne su iya kashe wutar rikici. Duba da yadda wasu irin kwamitocin da aka kafa a baya a Afirkla suka gaza yin tasire wajen warware rigiginmu
Shin Klub din Bayar Munich na Jamus na da matsala ne da Ruwanda. Wannan shi ne take da Jaridar Bild Online ta bude sharhinta da shi a kan Kwango wacce ta ce Klub din Bayern na Jamus an kaishi bango saboda daukar nauyi da yake na shaanin wasanni da yake ba da gundumowa ga Ruwanda,duk da halin da ake ciki na keta doka da Ruwandar ke yi na bai wa yan tawayen M23 goyon baya.
Ofishin ministan harkokin waje na Jamus ya yi kakkausa sukan a kan hakan tare da yin kira wa Ruwanda ta janye dakarun ta daga Kwango domin muntata doka ta kasa da kasa da kuma ganin klub din na Bayern ya daina ba da tallafin sa wa Ruwanda
Abin da ke da mahimmanci game da batun shine babban kocin Bayern Munich Vincent Kompany dan shekaru (38) yana da tushen tsatzso daga Kwango kuma ya yi magana game da yadda yake alfahari da ita da yadda yake son zaman lafiya a kasar. Wanda aka haifi mahaifisa a gabashin Kwango a Bukavu a Yankin Kivu kafin ya tsere hijira zuwa Beljiyam a lokacin mulkin Mubutu saboda matsin lamba
Jaridar Suddeutsche Zeitung a sharhin da ta buga ta aza ayar tambaya ce kan cewar anya kuwa ba akwai barazanar kisan kare dangi ba a Sudan. Hari an sansanin ‘yan gudun hijira na Zamzam inda aka kashe jamaa da dama
Sansanin Zamzam da ke kudu da garin El-Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa, yana dauke da mutane akalla rabin miliyan. Dakarun FSR sun kai hari, a kan sasanin an kwashe kwanaki biyu ana gwabza fada a sansanin tsakanin dakarun FSR da sojoji gwamnati, da kuma mayakan sa-kai. Ana zargin bangarorin da ke fada da kai hare-hare bama-bamai a asibitoci da kuma kan fararan hula Wadanda ta ce daga kowane bangaran na gwamnatin da ‘yan tawaye al'ummar na fuskantar barazana.
Za mu karkare sharhin ne da jaridar Frankfurter Allgemeine wacce ta buga takenta da cewar har zuwa zuwa Yuro 15,000 kowane iyali a Senegal zai iya samu. Wadanda aka azabtar da su a baya-bayan a lokacin mulkin Macky Sall.
A karshen watan Janairu, gwamnatin Senegal ta sanar da shirin na biyan diyya ga wadanda aka zalunta a siyasance. A cewar ma'aikatar kula da jin dadin rayuwar iyali ta Senegal, kowane iyali inda aka samu mutuwa a sanadin boran da aka yi, na yaki da tazarcen da Macky Sall ya so ya yi.
Zai samu kimani miliyan goma na kudin CFA daidai da EURO dubu 15, wadanda kuma suka samu rauni za su samu Jika 500 na CFA kudin magani kwatankwancin EURO 765. Abim da ake ganin tamkar na goro ne ga irin fafutukar da suka yi wanda shirin ke shan suka daga 'yan adawa dake korafin cewar an yi tuwa na mai na.