Rikicin siyasar Nijar ya fara ɗaukar sabon salo
January 18, 2011Wata sabuwa ta ɓullo a jamhuriyar Niger, inda kotun tsarin mulkin ƙasar ta yi watsi da shawarar da shugaban ƙasa janar Salou Djibo ya gabatar mata, inda ya nemi a yi ƙarin wa'adin kwanaki uku domin baiwa jam'iyyun siyasa damar gyaran takardun 'yan takarar su na majalisar dokoki waɗanda kotun ta yi watsi da su a karshen makon jiya. To sai dai tuni wasu jam'iyyun suka fara mayar da martani dangane da wannan dambaruwar siyasa da ƙasar ta Nijar ta faɗa. Wasu na ganin cewa batun soke sunayen 'yan takara da aka yi, indan ba'a kawo gyara ba, to hakan na iya kawo cikas ga zaɓen ƙasar.
Kuna iya sauraron sauti a ƙasa, cikin rahoton da waklin mu Gazali Abdou Tasawa ya aiko mana. Da kuma shiri na musamman kan siyasar Nijar wanda Usman Shehu Usman ya shirya.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Ahmadu Tijani Lawal