Rikicin Kwango na ci gaba da daukar hankalin Jaridun Jamus
May 2, 2025"Ba ma iya barci ko da na dare daya ne, ido a bude muke kwana" Da haka ne jarida Zeit Online ta bude labarin da ta wallafa a a kan rikicin yankin gabashin Kwango da yaki ci ya ki cinyewa. Jaridar ta ce a gabashin Kwango babu hukumar shari'a, babu 'yan sanda: Rashin bin doka da oda ya zama ruwan dare a yankin. Tare da taimakon ruwanda, mayakan M23 sun kafa gwamnatin kama-karya.
Karin Bayani: Mai ya hana kawo karshen rikicin Kwango?
Akalla ana gudanar da tattaunawar zaman lafiya: Inda ake sa ran Ruwanda da Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango su gabatar da taswirar yadda za a gudanar da gabashin kasar. A yankin da ake fama da tashin hankali, sama da ‘yan bindiga 100 ne ke fafatawa da juna domin nemar wa ‘yan kabilarsu madafan iko. A halin yanzu, mayakan fafutuka na M23 sun kafa tsarin mulkin kama-karya a can. Ta fi ko wace kungiya mallakar makamai saboda taimakon da take samu daga makwabciyarta Ruwanda, M23 tana da makamai na zamani kuma tana da'awar kare 'yan kabilarta ta Tutsi, a gabashin Kwango.
A karshen mako ne dai ministocin harkokin wajen Kwango Thérèse Kayikwamba Wagner da na Ruwanda Olivier Nduhungirehe suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna a birnin Washington, D.C. Tun a shekara ta 2021 ne dai ake gwabza fada da kungiyar ta M23. Watanni biyu da suka gabata sun kwace manyan biranen lardunan Goma da Bukavu tare da nada nasu gwamnatoci.
"Lamura na kara tabarbarewa a Sudan ta Kudu" Wannan shi ne taken sharhin da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta wallafa a kan rikicin da ke kunno kai a Sudan ta Kudu. A cewar Majalisar Dinkin Duniya tashe-tashen hankula na iya kara kamari, shugabannin kabilun yankin na kokarin sasanta rikicin cikin lumana.
Karin Bayani: Fargabar rinchabewar rikicin Sudan ta Kudu
Tun da aka kafa kasar a shekarar 2011, Sudan ta Kudu ba ta taba samun cikakken zaman lafiya ba. Yakin basasar na shekaru bakwai ya zo karshe a shekarar 2018 tare da yarjejeniyar raba madafun iko tsakanin manyan kabilun kasar biyu wato Dinka da Nuer. Sai dai tun daga wannan lokaci ana ci gaba da samun tashin hankali a cikin gida.
Sojojin gwamnati na fafatawa da mayakan 'yan tawaye a sassa da dama na kasar, kuma an harbo wani jirgin sama mai saukar ungulu na Majalisar Dinkin Duniya a farkon watan Maris. Shugaba Salva Kiir wanda dan kabilar Dinka ne, ya sa aka kama mataimakinsa Machar wanda dan kabilar Nuer ne.
Majalisar Dinkin Duniya na gargadin cewa sannu a hankali yakin basasa na iya sake barkewa a Sudan ta Kudu. Ta yaya za a iya hana hakan? Akwai tsarin kotuna na karkashin bishiyoyi, da ake gani za su iya taimakawa wajen daidaita kasar. Daya hanyar kuma ita ce, al'ummar kasa su ki komawa yaki.
Karin Bayani:Sudan ta Kudu: Riek Machar na fuskantar daurin talala
Zamu karkare shirin na wannan makon da jaridar Süddeutsche Zeitung ta wallafa. Sojoji da mayakan RSF na amfani da jiragen sama marasa matuka akai-akai. Ba wai kawai suna kai hari ga abokan gaba ba, har ma suna tsoratar da jama'a.
Dubban daruruwan mutane na cikin firgici babu inda za su fake: Mayakan kungiyar RSF sun yi luguden wuta tare da kutsa kai cikin katafaren sansanin Zamzam na 'yan gudun hijira a yankin Darfur na kasar Sudan, inda suka kashe daruruwan mutane. Kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar, maharan sun kuma yi amfani da wani nau'in makamin da a yanzu ake yawan amfani da shi a Afirka wato jirage marasa matuka.
Tun a watan Afrilun shekarar 2023, sojojin Sudan (SAF) da mayakan sa kai na Rapid Support Forces (RSF) ke fafatawa don samun galaba, tare da samun makamai daga wasu kasashe.