SiyasaAfirka
Rikicin kabilanci a Ghana ya halaka mutane sama da 30
September 4, 2025Talla
Rikicin kabilanci a kasar Ghana ya janyo asarar rayukan mutane 31, tare da raba mutane kusan 50,000 da gidajensu.
Sanarwar hukumomin Ghana a wannan Alhamis ta ce mutane 13,253 ne suka haure zuwa makwabciyar kasar Cote d'ivore, don tsira da rayukansu.
karin bayani:Gargadi ga masu ikirarin karbar wahayi a Ghana
Ministan harkokin cikin gida na Ghana Mubarak Muntaka ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP rawaito.