Rikicin jam'iyyar Labour na barazana ga takarar Peter Obi
April 8, 2025Jam'iyyar adawa ta Labour ta dare gida biyu ne sakamakon jayayya a kan halascin shugabancinta a karkashin Julius Abure. Bangarorin biyu na bai wa kansa irin fahimtara da suke so a kan wannan hukunci kotun kolin Najeriya. Wannan ya sanya nuna wa juna 'yar yatsa da ma tsayuwar gwamin jaki, kamar yadda Umar Faruq da ke zama sakataren jam'iyyar Labour ya bayyana.
Karin bayani: Rikicin jam'iyyar Labour ya dauki wani salo a Najeriya
Tun bayan kammala babban zaben Najeriya ne aka tsinci shugabanin jam'iyyar da kuma dan takarar neman shugabancin kasa a zaben 2023 a rana, inda tun suna yi a cikin gida har ta kai su ga kama hanyar kwance wa juna zani a kasauwa. Mr Peter Obi dai, shi ne tauraruwar da ta haska jam'iyyar Labour a zaben da aka gudanar inda ta zo a mataki na biyu. A yayin da wannan ke faruwa, akwai tsoron illar da rikicin zai yi wa Peter Obi, wanda a baya ya musanta yunkurin hadaka da wasu jam'iyyun adawa a Najeriya, a cewar Farfesa Abubakar Umar Kari da ke zama masanin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Abuja.
Karin bayani: Rikicin shugabanci a jam'iyyar Labour
Rikicin cikin gida na Labour, lamari ne mai munin gaske ga jam'iyyar ta ‘yan adawa wacce ya kamata ta maida hankali wajen shirya wa zabubbuka da tinkarar kalubalen da take fuskanta daga jam'iyya mai mulki. Sai dai sakataren yada labaru na bangaren Peter Obi mai suna Ibrahim Ismail Umar na cike da kyakyawan fata ga LP. Tun kafin wannan lokaci dai, jam'iyyar Labour ta ce babu batun bai wa duk wani dan jam'iyyar takara neman shugabancin Najeriya kai tsaye, wanda a kaikaice ta janye tayin da ta baiwa Peter Obi.