Rikicin India da Pakistan na yin kamari
April 24, 2025Talla
Wannan matakin na zuwa ne bayan da India ta zargi Pakistan da hannu a harin 'yan bindiga da ya hallaka mutane 26 yawancinsu 'yan yawon bude idanu a yankin Kashmir wanda kasashen biyu suka dade suna takaddama a kansa
Hukumomin India sun ce daga ranar lahadi za su soke dukkan izinin Viza da suka bai wa 'yan Pakistan tare da umartar duk 'yan Pakistan da a suke cikin India su bar kasar kafin karewar wa'adin Vizarsu.
Kasar ta kuma sanar da daukar wasu matakai da suka hada da rage yawan ma'aikatan diflomaisyya da kuma rufe kan iyakar da ke tsakanin kasashen biyu.
A nata bangaren Pakistan ta rufe sararin samaniyarta ga dukkan jiragen sama mallakar India tare da dakatar da dukkan harkokin kasuwanci da India.