Rikicin a jam'iyyar adawa ta SDP da ke Najeriya
May 20, 2025
Ana jayayya tsakanin sassan jam'iyyar bisa wasu nade-naden mataimaka na shugaban jam'iyyar guda biyu a tsakanin sakatare da shugaban jam'iyyar na kasa. A baya dai ana yi mata kallon jam'iyya guda daya da ke da sigar tsafta cikin gida tsakanin jam'iyyaun adawa na Najeriya
SDP na zaman daya tilo a cikin manyan jam‘iyyun Najeriya guda hudu dake da wakilai a majlisun tarayya da bata da rikici. Amma rika kallonta da kimar yiwuwar mattatara ga masu adawar dake bukatar kai karshen mulkin APC ta masu tsintsiya. Kafin wani sabon rikicin dake jawo kace nace tsakanin shugaban jam'iyar Shehu Gabam da kuma sakatarensa Olu Ogunleye.
Karin Bayani: Najeriya: Ina makomar tsarin karba-karba?
A cikin makon jiya ne dai Ogunleye ya sanar da nadin wasu mataimaka guda biyu na shugaban jam'iyyar sassan arewacin kasar da kudancinta. Nadin kuma da shugaban jam#iyyar yace akai a kasuwa. Dr Sadiq Abubakar dai na zaman daya a cikin mataimakan guda biyu da zai lura da sashen arewacin kasar, da kuma ya ce yunkurin adawa da shugaban jam'iyyar babu hurumin hakan.
Duk da cewar hatsaniyar cikin SDP na da sigar gwagwarmaya ta neman ikon jam'iyyar, ana dai kallon sabon rikicin na iya taimakawa APC yar mulki a kokarin dorawa zuwa gaba cikin batu na mulki na kasar. Rushewar SDP na iya kai wa ya zuwa ci baya cikin gidan na adawa inda daukacin jam'iyyu hudun da ke tunani na hadewar wuri guda domin babban yakin na adawa ke fuskantar rudani.
Kafin yanzun dai an nisa a cikin hayaniya walau cikin gidan PDP ta adawa ko jam'iyyar Labour da ke da shugabanni dai dai har guda uku, da ma NNPP ta masu kayan dadin da ke da shugabanni biyu cur.