Kamaru: Sabuwar dambarwa kan zaben 2025
July 17, 2025Ministan yankunan Kamaru Paul Atanga Nji ya tabbatar da cewa jam'iyyun siyasa da suka kaurace wa zaben kananan hukumomi da na 'yan majalisa na 2020 ba za su shiga zaben shugaban kasa na 2025 ba.
Kalaman ministan na nufin kawar da 'yan adawa irin su Farfesa Maurice Kamto. Ministan ya bayyana kaurace wa zaben da cewa wani yanayi ne na bakin ciki.
Karin Bayani:Shugaba Paul Biya zai sake takara
Sai dai masana harkokin shari'a kamar Barista Oumarou Zakari lauya a babbar kotun Bamenda da ke arewa maso yammacin kasar ya ce Paul Atanga Nji ba shi da hurumin yanke irin wannan hukunci.
''Game da zaben da za a gudanar a 2025, shi ministan harkokin cikin gida yana da nasa ka'ida amma bai da karfin ya ce wane ba zai tsaya takarar zabe ba, wanda yake da hurumin cewa Maurice Kamto ba zai tsaya ba ita Elecam, domin Elecam ce ke da hurumin duba wane nene ya cancanta ya tsaya zabe ko ba zai tsaya ba''
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da Maurice Kamto ya sanar da cewa, a hukumance zai gabatar da takararsa a wannan Juma'a a ofishin ELECAM da ke birnin Yaoundé, don haka zai bude hanyar da za ta iya taka rawa a fagen siyasa da shari'a
Wannan al'amari ya haifar da damuwa game da rashin adalci ciki tsarin zabe inji Yahya Ahmed mataimakin shugaban jam'iyyar Action da ke adawa da mulkin Paul Biya
Karin Bayani:Kamaru ta sanar da ranar zaben shugaban kasa na 2025
''Mu 'yan adawa ba za mu yarda da haka ba, bai yi adalci ba, saboda shugaban kasa ba shi da karfin ajiye takardunsa na takara, wasu kuma a hana su tsayawa, to wannan abu ne da yake taimakawa wajen ta da zaune tsaye kuma ba za mu yarda da hakan ba''
Ministan ya gayyaci gwamnoni da masu ruwa da tsaki akan harkokin tsaron kasar inda ya ce za a tsaurara matakan tsaro domin ganin cewa an yi zabe cikin kwanciyar hankali
Karin Bayani:Kamarun: Biya ya gargadi 'yan adawa da su guji tayar da rikici
''Kamaru ba ta girgiza a lokacin zaben 1992 ba, ba wannan karon ba ne za ta girgiza kafin da bayan zabe 2025 ba, saboda shugaban kasa na kokarin sanya kwanciyar hankali, za mu karkafa tsaro kafin da bayan zaben shugaban kasa, ba za mu yarda da kalaman kiyayya da kabilanci ba za a hukunta duk wanda aka gano da wadannan laifukan ba tare da an tausaya ba''
A wannan rana sakataren jam'iyya mai mulkin Kamaru RDPC da daraktan ofishin fadar shugaban kasa suka mika takardar takarar Paul Biya ga hukumar zabe ELECAM.