Rikici ya barke tsakanin kasashen AES da kungiyar UEMOA
July 15, 2025Wannan sabon takun saka dai ya taso ne a lokacin taron majalisar ministocin kasashen na UEMOA da ya gudana a birnin Dakar na Senegal, bayan da shugabannin kungiyar suka haramta wa kasar Burkina Faso karbar shugabancin karba-karba na kungiyar da ya kawo kanta a wannan karo kamar yadda dokar tsarin tafiyar da kungiyar ta tanada.
Wasu dai 'yan kasashen na AES da dama sun zargi kungiyar ta UEMOA da yin karan tsaye ga dokokinta ta hanyar haramta wa Burkina Faso karbar shugabancin.
To amma Malam Issoufou Boubacar Kado wani mai sharhi kan harkokin tattalin arziki da siyasa a Nijar na goyon bayan kungiyar ta AES na ganin kamata ya yi kasashen na AES su dauki kuzarinsu su fice daga kungiyar ta UEMOA baki daya.
Wannan takun saka na zuwa ne a daidai loakcin da al'ummomin kasashen na AES ke bai wa shugabanninsu kwarin gwiwar ficewa daga tsarin na CFA domin samar da kudi nasu na kansu.
To sai dai Dokta Soly Abdoullahi masanin ilimin tattalin arziki a Nijar da shi ma kuma ke goyon bayan shirin kasashen na AES na kirkirar kudi na kansu, ya ce akwai bukatar yin taka tsantsan a cikin lamarin.
Yanzu dai jama'a sun zura ido su ga ko bayan ficewa da zauren taron majalisar ministocin na UEMOA za su dauki matakin ficewa daga kungiyar baki daya domin dukufa ga kera kudaden nasu na kansu, ko kuma za su mazayo ne su ci gaba da gwagwarmayar samun ‘yancinsu a cikin kungiyar ta UEMOA.