Rigimar takara bisa mukami a gwamnatocin Najeriya
April 28, 2022Kama daga kwamishinoni ya zuwa ragowar masu rike da mukamai na siyasa dai, daruruwan naddadu a jihohi ne dai ke tururuwar ajiye aiki da nufin taka rawa a zabukan tarrayar Najeriyar da ke tafe, wani abin da ke zaman kokarin bin umarnin dokar zabe. To sai dai kuma can a bangaren tarraya, abokan takun nasu irin na ministoci da ma ragowwa na jami'ai na gwamnatin tarrayar na ci gaba da kunne irin na kakar shegu bisa sashe na 84 na dokar zabe ta kasar.
Cikin tsakiyar rikicin dai na zaman fassara ta sashe na 84 na dokar zabe ta shekarar 2022 da ya yi karo da kundin mulkin tarrayar Najeriyar sannan ke neman gwara kai cikin fagen siyasa ta kasar yanzu. Chris Ngige dai na zaman daya a cikin masu neman takara ta shugaban kasar cikin inuwar jam'iyyar APC mai mulki, daya kuma a cikin ministocin gwamnatin tarrayar.
“Wannan sashen doka da majalisar tarayya ta kafa a cikin dokar zabe watau sashe na 84 karamin sashe na 12, an soke shi cikin hukuncin wata kotu. Kuma yanzu an daukaka shari'a, amma ya zuwa yanzu komai lalacewar hukuncin, dole ne a yi masa biyayya har sai in wata kotun ta sauya shi.”
Kokarin bin doka ko kuma kokari na siyasa dai, daya bayan daya gwamnoni a jihohin kasar 36 suka rika neman saukar jami'ai na gwamnatin da ke a jihohin nasu da nufin tunkarar zaben a wani abun da ke zaman yunkuri na kauce wa fushin alkalai.
Barrister Buhari Yusuf dai na zaman wani lauyan da ke zaman kansa a Abuja, da kuma ya ce ba hujja ga jami'an tarrayar cigaba da zama bisa kujerun nasu a cikin tsarin da kasar ke tafiya kai yanzu.
Kaiwa ya zuwa asarar zabe ko kuma kokari na korar duna, ana dai kallon sauka ta ministoci na gwamnatin tarrayar, na iya rage karfi ga Abujar cikin gwagwarmayar neman mulki na kasar a badi.