An kai tagwayen hare-hare a Nijar
March 16, 2021Mahukunta a jamhuriyyar Nijar, ba su kai ga tantance adadin wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon wasu tagwayen hare-hare da ake ganin na ta'addanci ne aka kai a wani yankin kasar da ke kusa da Mali. Wasu mazauna garin Banibangou na yankin Tillaberi, sun sheda yadda wasu fasinjojin cikin motar safa, kimanin ashirin suka mutu a sakamakon harin 'yan bindiga akwai kuma wasu talatin da suma suka mutu daga wani hari da aka kai kan kauyensu a jiya Litinin.
Hare-haren mayakan Boko Haram daga Najeriya dana Tuareg a kasar Mali sun yadu sannu a hankali zuwa jamhuriyyar Nijar da ke cikin kasashen G5 Sahel. Rundunar sojin kawance da suka hada dana Faransa sun shiga aikin fatattakar mayakan da suka mayar da yankin tungarsu, kawo yanzu rundunar ba ta kai ga samun nasara ba ganin yadda mayakan ke kai hari na kwanton bauna dana sari ka noke suna barin jama'a cikin yanayi na jimami.