Rawar da ƙungiyar Super Falcons ta Najeriya take takawa
June 30, 2011'Yan mata matasa masu tarin yawa dake fatan wata rana su wakilci ƙasar su a wasannin ƙungiyar ta Super Falcons, yanzu haka suna baiyana fatan ƙungiyar zata yi nisa a wasnnin cin kofin duniya na mata dake gudana yanzu haka a nan Jamus. Yanzu haka a birnin Fatakwal, ana gudanar da wani gagarumin biki na kwallon kafa na mata matasa.
A birnin na Patakwal dai, mai koyar da 'yan wasan mata matasa, Raphael Agetu ya tara 'yan wasan sa domin samun horon da shi ne na ƙarshe kafin a fara gagarumin bikin na wasan ƙwllon ƙafa a wannan birni. Nan da makonni biyu masu zuwa ko da shi ke 'yan matan ba zasu yi takarori na neman ɗaukar kofin duniya ba ne, amma Raphael Agetu ya ce 'yan wasan sa wajibi ne su yi bakin ƙoƙarin su idan suka shiga filin wasa.
Ya ce a yau, ina ɗauke da littafi na, zan kuma lura da irin yadda kowace cikin ku take maida hankali. Sai wadda ta nuna ƙwazo ne zan sanya ta a fili idan aka zo wasa. Idan kuka maida hankali, ni ma zan maida hankali in rubuta sunayen ku cikin littafi na. Idan kuma kuka nuna sanyin jiki, ni ma zan yi sanyin jiki wajen rubuta ku a littafin nawa. Da fatan kun ji abin da na fada.
'Yan wasan matasa sun gane kuma sun fahimci muhimancin wannan gasa, inda kowace daga cikin jihohin ƙasar 36 ta tura 'yan wasan ta matasa da suka fi ƙwarewa a fannin ƙwallon ƙafa. 'Yan wasa da dama ba su ɗora hankalin su ga samun nasarar gasar ba, amma maimakon haka, sun fi baiyana fatan wasu ƙwararru dake sa ido a ƙwazon su, zasu ɗauke su, inda zuwa gaba zasu maida ƙwallon ƙafan mata ya zama sana'ar su da zasu dogara da ita. Ita ma Nkiruta Timothy dake cikin tawagar 'yan wasan da suka fito daga Abuja tana da irin wannan fata.
Ta ce mafarki na shi ne in zama na fi kowa cin ƙwallo a wannan gasa, saboda ni yar wasan gaba ce, saboda haka mafarki na shi ne in ta jefa ƙwallo a gidan abokan karawar mu. Ina ganin abin da Messi yake yi, kuma ina ganin abin da Ronaldo yake yi. Ina matuƙar sha'awar yadda suke cin ƙwallo. Ni ma ina so in riƙa cin ƙwallo kamar su.
Irin wannan ƙarfin zuciya da hangen nesa ba sabon abu ba ne a tsakanin 'yan wasan ƙwallon ƙafa mata a Nijeriya. Dalilin haka shi ne nasarorin da ƙungiyar mata ta ƙasar, wato Super Falcons take samu. 'Yan matan na Nijeriya dai su ne zakarun nahiyar Afrika baki ɗaya. Ƙungiyar ta Super Falcons ta kan nuna wa matasan cewar su ma dai suna iya samun nasarori su kuma nuna cewar ƙwallon kafa na mata shi ma ba a baya yake ba, saboda kamar yadda Nkiruta Timohy ta nunar, har yanzu ana ci gaba da ɗaukar ƙwallon ƙafan mata ba 'a bakin komai ba.
Ta ce mahaifi na musamman ya nuna adawar sa kan ƙwallon ƙafan na mata, saboda baya son yayan sa su riƙa nuna halittar jikin su, ko su sanya irin waɗannan tufafi 'yan ƙanana.
To amma a yau, mahaifin nata yana alfahari da ita, inji Timothy. Bayan neman kwatanta ƙwazon 'yan wasa dake gaban su, matasan na Nijeriya suna kuma da wani burin dabam: wannan wasa ya zama masu wata hanya ta samun kuɗi. Wannan dai al'amari ne mai wahala, saboda ƙwallon ƙafan mata a Nijeriya ba'a tanadar masa isasshen kuɗin da ya dace.
Adanna Gloria Nwaneri, wadda ita ma mai koyar da wasan na ƙwallon ƙafa ce, ta ce ba su da waɗanda suke ɗaukar nauyin su ta hanyar taimakon kuɗi kamar yadda 'yan wasa maza suke da su. Saboda haka ne ƙwallon ƙafar mata, maimakon ya ci gaba, sai ma komawa baya yake samu. To amma duk da haka, Adanna Gloria Nwaneri ta ce tana yi wa mai koyar da Super Falcons, Eucharia Uche fatan alheri, musmaman a karawar da 'yan wasan na Nijeriya zasu yi da Jamus.
Mawallafi/Katrin Gänsler/Umaru Aliyu
Edita: Ahmad Tijani Lawal