Rashin tabbas a dangatakar Rasha da Amirka
October 23, 2011A matsayin martaninta ga matakin Amirka na hana wa jami'anta visa, Rasha ita kuma ta kakaba haramcin ba da da visa akan wasu jami'an Amirka. Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta fid da jerin sunayen wasu Amirkawa da za ta hana musu shiga cikin harabarta. Wata sanarwa da aka bayar ta nunar da cewa wadannan sun haɗa ne jami'an Amirka da ake zaton suna da hannu wajen gallaza wa Rashawa da kuma zargin azabtarwa da kashe farar hular da ake tsare da su a ƙasashen Iraki da Afganistan.
Wannan mataki na Rasha dai martani ne ga matakin Amirka na haramta visa ga wasu jami'an Rasha da ake zaton suna da hannu a cikin kisan da aka yi wa lauya Sergei Magnitsky a gidan wakafi. Mutuwarsa da ta faru a shekaru 2009 ta janyo zargin da ake wa Rasha na take hakkin bil Adama. Wannan takaddamar dai aba ce da ka iya jefa dangatakar Rasha da Amirka a cikin wani hali na rashin tabbas a daidai lokacin da dukansu biyu ke shirin gudanar da zaɓen shugaban kasa a shekara mai zuwa.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Zainab Mohammed Abubakar