Rashin daidaituwar ba da ilimi a Kenya
June 21, 2012Kusan rabin al'ummar kasar Kenya gaba ɗaya ƙananan yara ne da matasa. Ko wace mace a ƙasar takan haifi 'ya'yan da basu kasa guda huɗu ba a rayuwarta. Da yawa daga cikin waɗannan yara sukan daina zuwa makarantun farko na firamare, tun kafin su kai misalin aji takwas, saboda a makarantun suna bukatar kayan tufafi da takalma da litattafai da kayan rubutu kamar alƙaluma da takardu, waɗanda abubuwa ne da iyalai da yawa ba za su iya saya wa 'ya'yan nasu ba saboda tsada. Makarantun gwamnati sukan cika da yara, inda ajiya yakan kasance dauke da yara akalla arba'in a ciin sa, tare da malamai da ba'a biyan su albashi, ko wadanda albashin su bai taka kara ya karya ba. Babu kujeru ko bencin zama, babu littafan karatu babu alluna, yayin da mafi yawan yan makartantan sukan zauna a kasa. Makarantu masu zaman kansu a ɗaya hannun, suna da duka wadannan abubuwa da makarantun gwamnati suka rasa, amma su a kuma da tsada. Malaman dake koyarwa a cikin su, suna samun albashi mai kyau, suna kuma da horon da ya dace. Bayan yaro ya kare karatun aji takwas, akan shirya jarrabawa ta kasa baki daya, inda sakamakon da aka samu yakan baiwa wadanda suka sami nasara damar shiga makarantun sakandare. A nan ma, akan lura da cewar yaran dake zuwa makarantu masu zaman kansu sun fi kokari, sun kuma fi samun damar cin jarrabawar.
Ko wane yaro dake zuwa makarantar sakandaren gwamnati ya kan kashe abin da ya kai Euro ɗaya ne a kullum, abin da ya gagari iyalai da dama a ƙasar ta Kenya, saboda misalin kashi ɗaya cikin kashi biyar na yan kasar suna rayuwarsu ne ba tareda abin da ya kai Euro daya a kulum ba, yayin da iya
Al'ummar ƙasar Kenya din suna dora muhimmanci mai yawa kan fannin ilimi. Saboda haka ne iyaye masu tarin yawa suka gwammace su daukarwa kansu bashin da yafi karfin su ko su sayar da gonaki ko filayen da suke mallaka, yadda yaransu zasu sami ilimi mai zurfi kuma mai nagarta. Manyan makarantu da jami'oi suna kokarin cimma biyan bukatun neman ilimi a kasar ta hanyar baiwa ɗalibai damar karatu na gajeren lokaci a fannoni da dama domin samun takardun shaidar ilimi mai zurfi. To sai dai abin baƙin ciki shine, mafi yawan takardun shaidar da ɗaliban sukan samu, basa dacewa da bukatun sauran ƙasashen duniya. A jami'oin ƙasar na gwamnati an sami ninkawar yawan ɗalibai masu karatu cikin su daga shekaru biyar da suka wuce zuwa yanzu. Hakan ya sanya idan har Kenya tana bukatar tabbatara da isassun malamai da zasu koyar a waɗannan jami'oi, tilas ko wace shekara ta samar da malamai masu ilimin Drs. A shekarun baya, ƙasar bata samar da masu wnanan ilmi mai zurfi da suka wuce 230 ba, inda ƙkungiyar musayar ɗalibai ta Jamus, wato DAAD ta taimakawa ilimin guda 50.
Musamman wannan matsala ta rashin samun ƙwarewa a manyan makarantun Kenya, tafi tsanani ne a tsakanin matasan ƙasar, saboda iyalai basa kashe kuɗi mai yawa a batun ilimin mata. KO da shike kwarewar da ake bukata daga mata kafin su shiga manyan makarantu bata kai ƙwarewar da ake bukata daga takwarorin su maza ba, amma mata yan kalilan ne suka karatu a jami'oi, inda yawan dalibai mata a manyan makarantun bai wuce kashi 40 cikin dari ba. Ganin cewar tun daga shekarun baya iyaye ne sukan biyawa yaransu kudin karatu a jami'oi, saboda haka ba ma sukan bmaida hankali ne ga zaben wadanda zasu biya suyi karatun ba, amma har hakan ya sanya ba'a cika maida hankali kan ilimin mata ba, saboda matan babu abin da ake sa rai daga garesu, illa su yi aure su hayaiyafa, su kula da iyalin su.
Sai dai kuma duk dfa wnanan banbanci a fannin samun ilimi a ƙasar ta Kenya, akwai tarihin neman iolimi na wasu ɗalibai maza da mata dake zama mai ƙarfafa gwiwa. Alal misali, wani matashi daga Nyeri ya kasance dauke da takardar shaida mafi kyau bayan ya kare karatun aji takwas. Hakan ya sanya wata cibiya ta ɗauki nauyin karatun sa na sakandare, kafin daga baya gwmanati ta dauki nauyin karatun nashi a fannin kimiyya da bincike a nan Jamus. Babban misali a game da nasarar baiwa mata ilimi kuma, ana iya ambata Auma Obama, wadda ya ce ga shugaban Amirka, Barack Obama. Bayan da ta sami takardar shaida mai kyau, kungiyar taimakon musayar dalibai ta Jamus, DAAD, ta dauki nauyin karatun ta a nan Jamus, ilimi bayan ta kammala, yanzu haka take aiki a ƙungiyar nan mai suna CARE International.
Mawallafi: Veweyen/Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal