Rashin sakin Bazoum ya hana armashin afuwar Tchiani
April 2, 2025A Jamhuriyar Nijar, na kasar da suka hada da wasu tsoffin mambobin gwamnatin hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum da kuma sojoji da ke tsare gidajen wakafi a bisa samunsu da laifin yunkurin juyin mulki a gwamnatocin da suka gabata.
Sai dai wasu ‘yan kasar ta Nijar na ganin rashin sakin hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum da mai dakinsa Hadiza ya rage wa matakin armashi musamman a game da shirin shugaban Tchiani na neman hada kan ‘yan kasa.
Babban Sakataren gwamnatin Nijar Mahaman Roufa'i Laouali shi ne yakaranto kudirin dokar yin afuwa ga wasu fursunonin siyasar kasar ta Nijar a gidan talabijin na kasana RTN. Matakin da ya shafi mutane 58 da suka hada da mambobin tsohuwar gwamnatin hambararren shugaban kasa Bazoum Mohamed irin su Malam Kalla Moutari da Mahaman Sani Youssoufou wato Abba dan tsohon shugaban kasa Mahamadou Issoufou. Akwai kuma tarin sojoji da ake tsare da su shekaru da dama a bisa samunsu da laifin yinkurin juyin mulki da suka hada da Janar Salou Souleimane da Lieutenant Ousmane Awal Hambali dukkaninsu na babbar rundunar soji ta kasa ta FAN.
Tuni dai wasu kungiyoyin kare hakin dan Adam suka fara nuna farin cikinsu da mataki tare kuma da yin hannunka mai sanda ga Janar Tchiani : Malam Soule Oumarou shi ne shugaban kungiyar FCR:
"Gaskiya wannan mataki da Tchiani ya dauka, mataki ne na gyara kasa da hadin kan ‘yan kasa domin ya zamanto an fuskanci alkibla daya, kuma kowa ya tsaya ya yi aiki don kasa fisabilillahi. Kuma shi shugaba Tchiani ya san cewa shi uba ne na kasa, duka diyansa muke. Kowa nashi ne, ya kamata ya yi taka tsan-tsan ga lamarin wasu da ke neman rura wuta, wadanda ke kokarin yi masa ingiza mai kantu ruwa, su tura shi rami, su ja baya su shiga nasu sha'ani"
Tuni kuma wasu iyalan sojojin da aka sako suka nuna farin cikinsu da matakin. Malam Aboubacar Idrissa mai Lakabin Abakaka, dan uwa ne ga Lietenant Ousmane Awal Hambali da aka sallama:
"Yau mu sai dai mu yi wa Allah godiya domin babbar rana ce wacce ba za mu taba mantawa da ita ba, game da sakin wannan dan uwa namu Lieutenant Ousmane Awal Hambali. Ya share shekara 10 da wata uku a gidan yari dabam-dabam. Kuma muna fatan Allah ya kiyaye gaba domin mu wanga abu da ya faru gare mu ko makiyinmu ba ma fata ya samu kanshi a ciki".
Sai dai wasu ‘yan Nijar din na ganin rashin sakin hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum da mai iyalinsa Hadiza ya rage armashin matakin afuwar da na shugaban kasa Janar Abdourahmane Tchiani. Docta Mayra Djirine wata ‘yar fafutika ‘yar Nijar da ke da zama a Faransa na da daga cikin masu wannan damuwa.
"Janar Tchiani in yana son a yi gafara ta tsakani da Allah a tsakanin ‘yan Nijar, to Bazoum ya kamata ya fara saki kafin ma ya saki wasu. Domin ko yana so ko ba ya so, Bazoum Aljanna ce mai masoya da yawa. Domin yanzu a Nijar har wadanda aka cusa wa ra'ayi na bata Bazoum da farko a yanzu sun gane. Yanzu masoyan bazoum kowace safiya karuwa ne suke. Kenan idan Tchiani ya saki Bazoum ne yake iya samun masu goya masa baya da yawa".
Sai dai ko baya ga shugaba Mohamed Bazoum da mai dakinsa, matakin sakin ya yi tsambaren sakin Malam Hama Adamou tsohon ministan cikin gida na hambararriyar gwamnatin Bazoum, da kuma Malam Moussa Tchangari dan jarida kuma dan fafutika kana shugaban kungiyar Alternative Espace Citoyen, mutanen da gwamnatin ya zuwa yanzu ba ta bayyana dalilin ware su daga cikin wadanda shugaban kasar ya yi wa afuwa ba.