Rashawa: An kori shugaban hukumar shige da fice na Saliyo
March 13, 2025Shugaban Saliyo Julius Maada Bio ya sallami shugaban hukumar kula da shige da fice ta kasar 'yan sa'oi bayan wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta da ya haska shugaban ya karbi kyauta daga hannun kasurgumin mai hada-hadar hodar iblis din nan na kasashen Turai Jos Leijdekkers da ake nema ruwa a jallo.
Karin bayani: Sabon shugaban Saliyo ya yi alkawarin hadin kan kasa
Jos Leijdekkers da ake yi wa lakabi da "Chubby Jos", na daga cikin jerin masu hada-hadar miyagun kwayoyi da sojojin kasa da kasa ke nema ido rufe, wanda kuma yake ci gaba da rayuwa a kasar Saliyo tare da mu'amala da manyan jami'an gwamnati ciki har da 'yar shugaban kasar.
Karin bayani: Kotun Saliyo ta wanke dan takarar adawa
Bankado bidiyon karbar kyautar da shafin nan na Follow the Money ya bankado ya harzuka al'ummar kasar har ma da 'yan adawa, inda jagoran adawa na Saliyo da ke gudun hijira a kasashen ketare Mohamed Mansaray, ya zargi gwamnatin Bio da bai wa gungun masu hada-hadar kwayoyi mafaka a kasar, ciki har da "Chubby Jos" dan asalin Netherlands da ake nema ruwa a jallo.