Rasha za ta bai wa kasashen AES tsaro mai karfi
April 5, 2025Rasha ta bayyana aniyar taimaka wa gwamnatocin mulkin soja a kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar, a bangaren karfin makamai da kuma horo a game da tsaro.
Ministocin ketare na kasashen uku dai sun ziyarci Rasha inda tun a ranar Alhamis suka fara ganawa da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov.
Rasha ta bayyana shirin kafa wata runduna mai dakaru dubu biyar da za su tare a yankin Sahel kamar yadda ta sanar tun cikin watan Janairu.
Kasahen uku na Sahel dai sun kafa kungiyarsu ta AES, bayan kifar da gwamnatocin fararen hula da suka zarga da rashin yin katabus wajen yaki da ta'addanci da sauran wasu matsalolin.
Nijar da Burkina Faso da Malin dai sun raba gari da sojojin Faransa da na wasu kasashen yammacin duniya, inda suka koma wa Rasha wajen neman taimako ta fuskar tsaro.