Rasha ta zargi Amirka da yi mata katsalanda
December 8, 2011Fraiministan Rasha, Vladimr Putin ya zargi Amirka da hanzuga zanga-zangar da aka fara tun kwanaki uku da suka gabata domin nuna rashin aimncewa da yadda zaben majalisar dokokin kasar ya gudana. Putin ya ce sakatariyar harkokin wajen Amirka, Hilary Clinton ta tabbatar da hakan a cikin kalaman da ta yi, yana mai zargin 'yan adawa da yin amfani da kudaden da suka samu daga ketare domin sauya sakamakon zaben da ya gudana a ranar 04.12-2011. Putin ya bukaci shiga tattaunawa tare da 'yan adawa amma ya bayyana cewa dakarun tsaro za su ci gaba da sa kafar wando daya da duk wanda zai taka doka. A ranar laraba 07-12-2011 sai da 'yan sandan Rasha suka yi arangama da masu zanga-zanga a biranen Moscow da St. Petersburg inda aka sake kame 'yan adawa sama da dari. Ga baki daya dai mutane sama da dubu ne dakarun tsaro suka kame a fadin kasar ta Rasha a yan kwanakin da suka gabata.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu