SiyasaTarayyar Rasha
Ukarine: Rasha na maraba da matakin sulhu
March 5, 2025Talla
Kakakin fadar Kremlin din Dmitry Peskov ta Rasha ya bayyana hakan sai dai ya ce, akwai alamun tambaya a batun tattaunawar. A cewarsa tun a shekara ta 2022 Zelensky ya sanya hannu kan wani kudirin doka, wadda ta haramta duk wani batun zama kan teburin sulhu tsakaninsa da Shugaba Vladimir Putin na Rasha. Zelensky dai ya ce a shirye yake ya yi aiki karkashin jagorancin Shugaba Donald Trump na Amurka, domin samar da zaman lafiya mai dorewa. Matakin Zelensky na zuwa ne kwanaki kalilan bayan wata ziyara da ya kai ofishin shugaban Amurkan, inda ya ayyana Putin a matsayin makashin al'umma kuma dan ta'adda.