Rasha ta soki Amurka kan jibge makamin roka a Japan
August 29, 2025Talla
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma'a, mai magana da yawun ma'aikatar, Maria Zakharova, ta ce wannan mataki wani sabon salon tayar da hankalin duniya ne daga Amurka. Ta kara da cewa Amurka na ci gaba da kara karfin makaman roka na kasa don tura su a sassa daban-daban na duniya.
Rahotonni sun ce Amurkan za ta dasa makaman rokan a yayin atisayen hadin gwiwa na Resolute Dragon a kasar Japan.
Rasha ta ce irin wadannan matakai da Amurka ke dauka ka iya kara dagula tsaro a yankuna da dama na duniya.