Rasha ta shiga ƙingiyar cinikayya ta Duniya
December 16, 2011Rasha ta shiga ƙungiyar cinikayya ta Duniya watau WTO, bayan shekaru 18 na tattaunawa, a yau ne wakilan ƙungiyar baki ɗayansu suka yi amanar amincewa da wannan ƙasa ta tsohuwar janhuriyar Soviet mai albartu masu ɗunbin yawa. Rasha dai ita ce ƙasa mai ƙarfin tattalin arziki data haɗe a wannan ƙungiya, shekaru 10 bayan shigar ƙasar China. Ƙungiyar tarayyar Turai da ke zama babbar aminiyar kasuwancin Rashan, ta yi maraba da sauyin da aka samu cikin hakokin haraji, wanda acewarta zai inganta fitar da kayayyaki daga ƙasar zuwa kasuwannin Duniya. Sai dai wani babban saɓanin ra'ayi akan kasuwanci tsakanin Amurka da Rasha, ya mamaye zauren taron kungiyar cinikayyar a birnin Geneva. Amurkan dai ta ce ba zata iya bawa Rasha sassaucin ƙungiyar cinikiyyar a yanzu ba, domin har yanzu majalisa bata amince da ita ba a ƙarƙashin tsarin dokar zamanin yaƙi. A ɓangarenta Rasha ta ce itama, ba zata aiwatar da ƙa'idojin ƙungiyar ba a harkokin kasuwancinta da Amurka. Ministan tattali na tarayyar Jamus Philip Roesler ya bayyana cewar shigar Moscow ƙungiyar ta WTO, kyakkyawan abu ne a ɓangaren ƙasashen biyu da ma ita kanta ƙungiyar cinikayyar.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman