Rasha ta sanar da musayar fursunonin yaki da Ukraine
July 4, 2025Kasar Rasha ta sanar da musayar fursunonin yaki da Ukraine, a matsayin wani bangare na yarjejeniyar da aka cimma a farkon watan Yuni a Istanbul, da ta gaza samar da wani ci gaba wajen warware rikici tsakanin kasashen biyu. Sai dai har yanzu, hukumomin Ukraine ba su ce uffan kan wannan sanarwar ba. Ita kuwa Moscow ba ta fayyace adadin fursunonin da aka saki ba.
Karin bayani: Ukraine da Rasha sun yi musayar fursunonin yaki 538
Tun dai kwanaki biyun da suka gabata ne Ukraine da Rasha suka amince da sakin dukkan wadanda suka jikkata a yaki tare da mayar da gawarwakin mayaka da aka kashe. Har yanzu dai ba a tsayar da ranakun tattaunawar zagaye na uku tsakanin sassan biyu ba. Amma Rasha ta yi watsi da duk wani shirin tsawaita zaman lafiya, tare da neman Ukraine ta mallaka mata jihohi hudu na kasarta, sharuddan da Ukraine ta ki amincewa da su.