SiyasaTarayyar Rasha
Rasha ta saka wa WhatsApp da Telegram takunkumi
August 13, 2025Talla
Rasha ta sanar da saka takunkumin takaita yin kira ta kafafen sadarwa na WhatsApp da Telegram, matakin da ke zama wani sabon abu bayan da a shekarun baya ta rufe wasu shafukan sada zumunta na kasashen yammacin duniya.
Kamfanin dillacin labaran Rasha Ria Novosti ya ruwaito ma'aikatar sadarwar kasar na cewa an dauki wannan mataki ne don dakile masu aikata miyagun laifuka ta kafar intanet.
Karin bayani: Amirka da Rasha za su yi maganin kutse
Mahukuntan Rasha dai na zargin wadannan kafafen sadarwar zamani da karfafa gwiwa ga masu aikata zamba cikin aminci da kuma yada ayyukan ta'addanci, yayin da wasu ke kallon matakin a matsayin tauye 'yancin walwala da fadar albarkacin baki.