Rasha ta kwace garuruwan Ukraine a wani sabon farmaki
June 9, 2025Rasha ta sanar cewa sojojinta sun kwace iko da wasu sabbin yankuna a gabas maso tsakiyar yankin. Kremlin ta ce tana fada a can ne domin samar da fagen daga kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka ambato Ma'aikatar Tsaron kasar na cewa.Dnipropetrovsk na kasar Ukraine.
Musayar fursunoni tsakanin Ukraine da Rasha na tafiyar hawainiya
Kafar yada labarai ta Reuters dai ba ta tantance sahihancin labarin ba ya zuwa yanzu amma Ukraine ta fada a karshen mako cewa ta na kan layi a gabashin Dnipropetrovsk. Rasha da Ukraine sun sabonta tattaunawa don samar da zaman lafiya tun a watan Mayu a kasar Turkiyya, to amma duk da haka yakin ya ki daina sanyi.
Rasha da Ukraine na tattaunawar dakatar da yakin da suke yi
Wani jami'in na Rasha ya ce shugaban kasar Vladimir Putin ya amince da wani gagarumin garambawul ga sojin ruwan kasar domin kara musu karfi.