Rasha ta kori jami'an diplomasiyyar Jamus
March 30, 2018Gwamnatin Rasha ta yi kira ga jami'an diplomasiyyar Jamus hudu da su bar kasar, jim kadan da gayyatan jakadun kasashen yammacin duniya tara a ma'aikatar harkokin waje da ke birnin Moscow. Ofishin da ke kula da lamuran Harkokin Wajen Jamus da ke Berlin ne ya bada wannan sanarwa, da ke zama ramuwar gayya ga matakin da wasu kasashe suka dauka na korar jami'an diplimasiyyar Rasha bisa zargin yunkurin kisan tsohon jami'in asirin Rasha Serguei Skripal.
Dama dai Rasha ta sanar da sallamar jami'an diflomasiyyar Amirka akalla 60 da na Holland hudu, sannan kuma ta dibar wa Birtaniya wa'adin wata guda don ta rage yawan jami'an diplomasiyyarta a Rasha. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadin cewar za a iya fuskantar dawowar yakin cacar baka tsakanin kasashen yammacin duniyar da Rasha sakamakon zargin yunkurin kisan da ke kara zama dalilai na wargaza alakar kasashen duniya da Rasha.