Rasha ta kai wa Ukraine gagarumin hari
September 7, 2025Hakumomin Ukraine sun ba da rohoton mutuwar mutane biyu bayan wasu jerin hare-hare da Rasha ta kai wa yankunan kasar da dama a cikin daren Asabar wayewar Lahadi.
Masu aiko da rahotanni sun ce an jiyo karar na'urorin alamta hari a fadin kasar, yayin da fadar mulki ta Kiev ta ce harin ya lalata wasu gine-ginen jama'a.
Wasu rahotannin kuma na cewa a hango gajimaren hayaki na tashi a wani ginin gwamnati a birnin Kiev, kafin jiragen kashe gobara su bi ta kansa suna watsa ruwa.
Gwamnan yankin Soumy mai iyaka da Rasha ya ce harin ya yi ajalin mutum guda a yankinsa tare da jikkata wasu mutanen da dama ciki har da wani yaro mai shekaru tara.
Hakazalika a yankin Japorijjia da ke kudu maso gabas da kuma yankin Kryvii da ke zama mahaifar shugaba Volodymyr Zelensky nan ma ruwan bama-baman na Rasha ya jikkata mutane da dama a cewar mahukuntan Ukraine.