Rasha ta kai harin da ya kashe fursunoni a Ukraine
July 29, 2025Kasashen Ukraine da Rasha sun zargi juna da hannu a hare-hare a kan gidan yarin da ke yankin Donetsk wanda Moscow ta mamaye, gwamnatin Kyiv ta ce an kashe sojojinta da dama da suka ajiye makamansu a tashar jiragen ruwa ta Mariupol a sansanin Olenivka.
Humumomin Ukraine sun ce wasu mutane 35 sun jikkata sakamakon harin bam da dakarun Rasha suka kaddamar cikin dare. An samu rahotannin wasu hare-hare guda takwas da suka hada da bama-bamai, wadanda suka lalata gidaje da dama.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya yi Allah wadai da harin, tare da cewa "laifin yaki ne". Sai dai Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sha musanta zargin kai irin wadannan hare-hare.
Sabbin hare-haren na zuwa ne sa'o'i bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya ba wa Moscow wani sabon wa'adi na kawo karshen mamayar da take yi a Ukraine, ko ta fuskanci sabbin takunkumi daga Washington.