Rasha ta gargadi Jamus kan bai wa Ukraine makamai
April 18, 2025Talla
Sabon makamin mai linzami samfurin Taurus KEPD-350 da Jamus ta kera na tafiyar kilomita dubu daya da 170 cikin sa'a guda, sannan kuma yana iya cim ma kilomita 500 daga inda duk aka harba shi.
Da sabon makamin dai Ukraine na iya cimma duk wani yanki na Rasha, yayin da take kokarin neman yadda za ta yi daga munanan hare-haren da Rashar ke tsanantawa a kanta.
Rasha dai ta ce za ta dauki taimakon wadannan makamai na Jamus ga Ukraine a matsayin shigar Jamus din cikin yakin kai tsaye.
Shugaban gwamnatin Jamus mai jiran gado, Friedrich Merz ya fada cikin makon da ya gabata cewar a shirye yake ya bai wa Ukraine sabbin makaman masu linzami.
Amma kuma ya fayyace cewa, zai yi hakan ne da hadin kan wasu kawayen Jamus din na Turai.