Shugaba Maduro na cigaba da samun goyon baya
March 3, 2019Talla
Sanarwar ta kara da bayyana fargabar asarar rayukan farar hula da zai biyo bayan matakin amfani da karfin soji da Amirka ta dauki aniya, a dalilin tirjiyar da shugaban kasar Nicolas Maduro ya ke cigaba da yi kan shigar da kayan agaji . A shekarar data gabata ne tawagar wasu al'ummar kasar Venezuela su ka yi kaura sakamakon fatara da talaucin da ya addabi kasar,lamarin da ya janyo kasashen ketare matsawa shugaba Maduro lamba kan laluben mafita.
Amirka na sahun gaba cikin kasashen da suke goyon bayan jagoran adawa Juan Guaido wanda ya ayyana kan sa a matsayin shugaban rikon kasar, yayinda kasashen Rasha da Chaina da Kuba da kuma Nicaragua suka dauki alwashin kare martabar Shugaba Nicolas Maduro har sai siyasar kasar ta daidaita.